1 Yuli 2021 - 11:57
Iran:An Nada Ghulam Husaini Muhsen Ajdi A Matsayin Sabokin Alkalin Alkalan Kasa

Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Imam Khaminae ya nada Gulam Husain Muhsini-Aje’ii a matsayin sabon alkalin alkalan kasar Iran.

ABNA24 : Majiyar ofishin jagaran juyin juya halin ne ya fidda wannan labarin a safiyar yau Alhami ta kuma kara da cewa jagoran ya bukaci sabon shugaban ya bada karfi wajen amfani da sabbin tsare-tsare na zamani wajen tafiyar da ayyukan sharia’a a kasar, ya kuma yi amfani da ma’aikata wadanda sukeka da kishin addini a cikin ma’aikatar da kuma sanya ida sosai a kan ayyukan ma’aikatar sa don fidda bara gurbi daga cikinsu.

Har’ila yau jagoran ya godewa tsohon alkalin alkalan sayyid Ibrahim Ra’isi kan irin gagaruwan sauyin da ya kawo a bangaren shari’a a kasar, ya kuma yi masa fatan alkhairi da nasara a sabon nauyin da aka dora masa na shugabancin kasar.

Daga karshe jagoran ya ce bisa doka ta 157 na kundin tsarin mulkin JMI na nada GulamHusain Muhsini Ajeii a matsayin alakalin alkalan kasar Iran.

342/